Al-Qeada: An Kashe Mataimakin Kwamandan

Wani rahoto ya bayyana cewa an kashe mataimakin Kwamandan Al-Qeada bisa umarnin Amurka a Tehran.

Ana zargin Abdullah da tarwatsa ofisoshin jakadancin Amurka a Tanzaniya da Kenya a shekarar 1998.

Hukumar yaki da ta’addanci ta kasar Amurka ta ce baya hannun hukumomin Kasar kuma gwamnati ta sanya tukuici ga duk wanda ya bada bayani kan yadda za a gano shi.

Mataimakin babban kwamandan Al-Qeada da aka gurfanar a Amurka a kan tarwatsa musu ofisoshin jakadanci a Tanzaniya da Kenya a shekarar 1998, rahotanni daga jaridar New York Times ta ruwaito ranar Juma’a cewa an kashe shi a sirrance tun cikin watan Agusta.

Abdullah Ahmed Abdullah wanda ke cikin jerin wanda rundunar FBI ke nema ruwa a jallo, an harbe shi kuma ya mutu a Tehran daga wasu jami’an Isra’ila a bisa umarnin Amurka, jami’ai na musamman sun tabbatar wa jaridar times.

Amurka, Iran, Isra’ila, ko Al-Qeada basu dauki alhakin harin da ya faru a ranar 7 ga watan Agusta lokacin tunawa da ranar fashewar bama-baman Afirka, The Punch ta ruwaito.

Babban shugaban Al-Qeada, Abu Muhammad Al-Masri, an kashe shi tare da ýar sa Miriam, tsohuwar matar Osama bin Laden, a rahoton jaridar Times.

Gwamnatin Amurka ta sanya ladan dala miliyan 10 ga duk wanda ya bada wani bayani da zai yi sanadiyar kama shi.

Abdullah shine “mafi wayo da kwarewa wajen tsara hare-hare, baya hannun Amurka ko kuma a hannun hukumomin ta”, kamar yadda yake a wata takarda ta hukumar yaki da ayyukan ta’addanci Amurka ta fitar a 2008, a cewar jaridar Times.

Tarwatsa ofisoshin jakadancin a Kenya da Tanzaniya a shekarar 1998 ya janyo mutuwar mutane 224 da kuma raunata fiye da mutane 5,000.

An gurfanar da Abdullah a gaban babbar kotun tarayya a Amurka sakamakon laifin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here