Rundunar Sojojin Sama ta Ragargaji Daruruwan ‘Yan Ta’adda

Rundunar OPERATION THUNDER STRIKE, tana cigaba da samun nasara a jihar Kaduna, inda suke ragargazar ‘yan bindiga ta jirgin sama.

A ranar 12 ga watan Nuwamban 2020, rundunar sojin saman ga samu nasarar kashe daruruwan ‘yan ta’adda, masu dauke da miyagun makamai.

Sun hango ‘yan ta’addan suna tafe a babura tare da shanu da tumaki masu yawa daga kauyen Dankolo suna tunkarar dajin kwiambana Rundunar sojin sama ta Operation Thunder Strike ta samu nasarar kashe wasu ‘yan ta’adda da suke dauke da miyagun makamai.

‘Yan ta’addan suna tafe ne a babura tare da shanu da tumakai a kauyukan Dankolo da Machitta da ke jihar Kaduna.

Rundunar sojin saman sun hangi ‘yan ta’addan ta wata na’ura mai hangen nesa, inda suka hangi ‘yan ta’addan a kauyen Kaboru, suna tunkarar dajin Kwiambana.

Kakakin rundunar sojin, John Enenche, ya sanar da hakan a wata takarda, wacce yace rundunar Operation THUNDER STRIKE ta ragargaji mafi yawan ‘yan bindigan da ke dajin Kwiambana a jihar Kaduna.

Kamar yadda yace, “Ragargazar ta auku ne a ranar 12 ga watan Nuwamba 2020, inda rundunar sojin saman ta samu nasarar kashe daruruwan ‘yan ta’addan da ke dauke da miyagun makamai suna tafe a babura da shanaye da tumaki masu yawan gaske, daga kauyen Dankolo suna tunkarar kauyen machitta.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here