Anyi Garkuwa da Wani Malamin kwalejin Nuhu Bamalli da Yara Biyu

Yan bindiga sun kai mamaya sashen gidajen malamai a makarantar kimiya da fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya.

Maharan sun sace malami daya da kuma yara biyu sannan suka harbi wani.

Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin inda tace a yanzu haka ta baza jami’anta domin ceto wadanda aka sace.

Yan bindiga a ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamba, sun kai farmaki kwatas din malamai na kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli Polytechnic da ke Zariya sannan suka sace wani lakcara da yara biyu, sannan suka harbi wani mutum daya.

An tattaro cewa wanda aka harban yana nan yana jinya a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello.

Da aka tuntube shi, jami’in hulda da jama’a na makarantar, Abdallah Shehu, ya ce yana cikin wani taro sannan ya yi alkawarin kira da zaran ya gama, Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai kuma, rundunar yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da lamarin cewa ya afku ne da misalin karfe 10:00 na dare, ta kara da cewa an garzaya da wanda ya ji rauni zuwa asibitin koyarwa na ABU don jinya.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige ya ce: “Muna kan lamarin. Yan sanda sun kakkabe yankin gaba daya sannan suna kokarin ceto mutanen.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here