Qudirin Tsohon Gwamnan Jahar Ekiti – Ayodela Fayose

 

Tsohon gwanan Ekiti, Ayodele Fayose ya bayyana wasu burika biyu da yake muradin cikawa a nan gaba.

Fayose ya ce yunkuri na gaba da yake son yi a rayuwarsa shine ya zama fasto ko kuma shugaban kasar Najeriya,

Ya ce ta hanayar zama mai isar da sakon Ubangiji ne kadai zai saka wa Allah kan ni’imomin da yayi masa a rayuwa.

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, wanda ya cika shekaru 60 a yau Lahadi, 15 ga watan Nuwamba, ya ce kudirinsa na gaba shine imma ya zama fasto ko kuma Shugaban kasar Najeriya.

Fayose ya yi magana ne a tashar radiyo ta Ekiti wato People’s FM, (104.19) kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito.

Sai dai kuma, tsohon gwamnan bai bayar da ainahin lokacin da zai nemi cika wadannan kudiri nasa ba, ko kuma wanne ne zai fara nema.

Ya ce Allah ya yi masa ni’imomi da yawa, don haka, hanyar da ta fi dacewa ya bi don gode yin godiya ga abubuwan da Ubangiji ya yi masa shine yin aikin Allah.

Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa ya yafe wa dukkanin mutanen da suka yi masa ba daidai ba, a yayinda yake kujerar mulki da bayan ya sauka.

Ya yi korafin cewa mutane da dama da ya aminta da su sannan ya daukaka su sun yasar da shi domin zama hadiman abokan hamayyarsa a siyasa, bayan ya bar karagar mulki.

Fayose ya kuma yi watsi da rade-radin cewa yana zawarcin zama sanata.

a ce ya tsani zama sanata wanda ke kafa dokoki da bangaren zartarwa ba za ta aiwatar ba.

A ranar Asabar, tsohon gwamnan ya wallafa wani hoto na takarar siyasarsa ta farko da kuma yadda ya fara lamarin siyasarsa a shafin Twitter.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here