Akwai Yiyuwar Masu Kasuwancin Man Fetur a Najeriya su Fara Daukowa Daga Kasashen Ketare

 

FCT, Abuja – Akwai alamun masu kasuwancin man fetur a kasar nan za su fara dauko man fetur daga kasashen ketare.

Matakin na zuwa bayan kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya bayyana cewa zai dauko fetur daga matatar Dangote idan farashinsa ya fi na kasuwar duniya arha.

Jaridar Punch ta wallafa cewa kalaman NNPCL na zuwa ne bayan shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce kamfanin mai na kasa kawai ya ke jira.

“Kowa ya dauko fetur daga Dangote,” NNPCL

Kamfanin mai na kasa (NNPC) ya bayyana cewa kowane dan kasuwa zai iya dauko fetur daga matatar Dangote ba sai an jira shi ba.

Legit.ng ta wallafa cewa NNPCL ya kara da cewa matatar Dangote za ta iya sayarwa duk dan kasuwar da ke son hulda da ita fetur.

Dangote: An magantu kan samuwar fetur

The Street Journal ta wallafa cewa ‘yan kasuwa sun bayyana damuwa kan rashin cimma matsaya tsakanin kamfanin NNPCL da matatar Dangote.

Yan kasuwar na bayyana cewa za su tafi neman man fetur a dukkanin wuraren da su ke da yakinin za su same shi da sauki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here