Emmanuel Macron: ƙasashen Musulmai Sun Fara ƙaurace wa kayan Faransa

Faransa ta bukaci kasashen Gabas Ta Tsakiya da ka da su amince da kiraye-kirayen ƙaurace wa sayen kayayyakinta.

Kauracewa kayayyakin da Faransa ke sayarwa wani ɓanagare na nuna fushi kan matakin Shugaba Emmanuel Macron na kare zanen fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta ce kiran da wasu masu tsattsauran ra’ayi ke yi na ƙaurace wa kayanta ‘ba shi da tushe’.
Tuni an fara cire kayan da Faransa ke samarwa a wasu shaguna da ke Kuwait da Jordan da kuma Qatar.

Haka ma an gudanar da zanga-zanga a Libiya da Syria da kuma Zirin Gaza.

Duk kuma hakan na faruwa ne tun bayan kalaman Mr Macron kan kisan gillar da a ka yi wa wani malamin makaranta da ya nuna wa ɗalibansa zanen Annabi Muhammad (SAW).

Me Shugaba Emmanuel Macron ya ce kan addinin Musulunci?

An ambato Shugaba Macron yana cewa “an kashe Samuel Paty ne saboda masu tsattsauran ra’ayin Islama na son ƙwace gobenmu, to amma Faransa ba za ta taɓa ba da gari ba kan zanen barkwanci.”

Bugu da ƙari, Mr Macron ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa “Ba za mu taɓa ba da kai ba.”

To amma Faransa na kallon kanta a matsayin ƙasar da al’umma ke da ƴancin faɗar albarkacin bakinsu kan abubuwa da dama.
,
Kasashen Musulmi na duniya da suka hada da Yammacin Turai na zargin Mr Macron da ƙoƙarin takura wa Musulmi ta hanyar halasta ƙyamar addinin Musulunci

Martanin kasashen Musulmi

Shugabannin siyasa a Turkiyya da Pakistan sun zargi Mr Macron da rashin girmama ƴancin addini da kuma shiga hakkin Musulmi a Faransa.

Ko a ranar Lahadi shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya shawarci Mr Macron da ya je a yi masa gwajin kwakwalwa kan yadda ya ke kallon addinin musulunci.

Hakan ya fusata Faransa, wanda ya sa ta janye jakadanta da ke Santambul.

Shi ma shugaban Pakistan Imran Khan ya zargi Macron da faɗa da addinin Musulunci kuma ya nuna ƙarara cewa ya jahilci wane irin addini ne.

Batun ƙaurace wa kayan Faransa shi ne maudu’i na biyu da ya fi jan hankali a Saudiyya, ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziki a Gabas Ta Tsakiya.

Dama tun kafin kisan Samuel Paty shugaba Macron ya sanar da tsauraran dokoki kan abin da ya kira “shirin masu tsattsauran ra’ayi kan Faransa”.
hoto,
Shugabannin siyasa a Turkiyya da Pakistan sun zargi Mr Macron da rashin girmama yancin addini da kuma shiga hakkin Musulmi a Faransa

Matakin ya ƙara sa Musulmin Faransa fargabar cewa gwamnati na yunƙurin yi musu katsalandan ga addini.

Haka ma Macron ya kuma ce Musulmin Faransa su miliyan shida na cikin haɗari yayin da addininsu ke ‘cikin rikici’.

Zanen Annabi Muhammad (SAW) ya kawo sauyi a siyasar Faransa.

Ko a shekarar 2015 an kashe mutum 12 a hari kan ofishin mujallar barkwanci ta Charlie Hebdo, wadda ta wallafa zanen a shafukanta.

Ba a Gabas Ta Tsakiya kaɗai ba, ko a sauran ƙasashen Musulmi na duniya da suka haɗa da Yammacin Turai ana sukar Mr Macron da ƙoƙarin takura wa Musulmi ta hanyar halasta ƙyamar addinin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here