Mata da ‘Ya’yanta Sun wa Matashi Duka Tare da Kona Shi a Kano
Rundunar ‘yan sanda a jahar Kano ta kama wata mata da ‘ya’yanta kan lakaɗawa wani matashi duka tare da kona shi da ruwan zafi.
Mata da yaranata sun ce sun ɗau wannan ɗanyen hukunci ne bisa zargin matashin da sace keken ɗanta.
Wannan lamari ya faru ne a unguwa uku da ke tsakiyar birnin Kano a arewacin Najeriya.
Yanzu haka dai ‘yan sanda sun kama matar da karin wasu mutum 3 da ake zargi da hannunsu a yanke wannan ɗanye hukunci.
Hotunan masu tada hankula sun nuna irin munin kunan da ke jikin matashi.
Wasu lauyoyi masu zaman kansu sun ci alwashin karbarwa matashin hakkinsa.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here