Shugaba Buhari ya Nada Dr Ezra Yakusak a Matsayin Shugaban NEPC
Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dr Ezra Yakusak a matsayin shugaban NEPC.
 Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.
Shehu ya ce nadin da aka yi wa Yakusak ya yi dai-dai da tanadin sashi na 7 (1) na dokar NEPC (Kafa), 1987.
Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dr Ezra Yakusak a matsayin babban direkta/shugaban Hukumar Bunkasa Harkokin Fita da Kayayyaki ta Najeriya (NEPC).
 Babban Mataimakin Shugaban Kasa na musamman a bangaren watsa labarai, Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook.
Shehu ya ce an nada Dr Ezra Yakusak ne a karon farko na wa’addin shekaru hudu kamar yadda ya ke a sashi na 7 (1) a dokar kafa NEPC ta shekarar 1987.
 A ruwaiyar jaridar Daily Trust, Shehu yace nadin zai fara aiki ne daga ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar 2021.
 Ya ce kafin nadinsa, Dr Yakusak, wanda ke da digirin digirgir a bangaren nazarin dokokin kasuwanci daga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria shine direktan sashin Dabaru da Manufofi na hukumar ta NEPC.
Mai magana da yawun shugaban kasar ya kuma ce wanda aka yi wa nadin ya taba aiki a matsayin sakatare na kwamitin gudanarwa na hukumar.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here