Bincike ya Nuna Mayaƙan Jihadi na Amfani da Makaman Sojin Najeriya,Chadi da Nijar

Wani rahoto ya ce makamai da yawa da aka ƙwace daga hannun ƴan bindiga a Nijar sun fito ne daga rumbun ajiyar makamai na wasu ƙasashen Afrika, wanda ke nuna cewa hukumomin ƙasashen na fuskantar ƙalubale na tabbatar da tsaron makamai a yankin.

Rahoton na wata cibiyar binciken makamai ta CAR da kamfanin dillacin labaran Reuters ya rawaito ya ce babu wata alama da ke nuna akwai gwamnatin da ke ba mayaƙa ko ƴan bindiga makamai da ke kai hare-hare a Nijar da Najeriya da Kamaru da Chadi.

Maimakon haka, binciken ya nuna cewa “tabbatar da tsaron kayan yaki na soja wani ƙalubale ga tsaron yankin, musamman wadanda ke yaki da ayyukan ta’addanci, a cewar rahoton.

Kungiyar ta ce ta gano makamai 165 da albarassai 6,243 a watan Oktoban 2019 da hukumomi suka kwato daga mayakan da ke da’awar jihadi a yankin Diffa, kudu maso gabashin Nijar.

Rahoton ya ce kusan kashi 17 na makaman sun fito ne daga Chadi da Najeriya da Nijar, yayin da kuma albararrai kashi 23 suka fito daga Najeriya.

Babu dai wani martani da ya fito daga gwamnatocin Najeriya da Chadi da Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here