Gwamnoni Uku na PDP Sun Shiga Ganawar Sirri da Olusegun Obasanjo
Ogun – Gwamnoni uku na jam’iyyar hamayya PDP sun shiga ganawar sirri da tsohon shugaban ƙasa a Najeriya, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Read Also:
Daily Trust ta rawaito cewa gwamnonin uku da suka sa labule da Obasanjo sune; Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, Seyi Makinde na jihar Oyo da gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai.
Sun dira laburarin tsohon shugaban ƙasan OOPL da misalin ƙarfe 6:40 na yammacin yau Litinin tare da jerin gwanon motoci, ba ɓata lokaci suka shiga ganawar kai tsaye.
Ƙarin bayani na nan tafe…