Babban Jigon APC a Zamfara ya Sauya Sheƙa Zuwa PDP

Yayin da jam’iyyar APC ke ganin ta fara gano bakin zaren rikicinta, wani jigo ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP mai adawa

Tsohon babban daraktan First Bank PLc, Dakta Dauda Lawal, bayan komawa PDP ya ayyana kudirin tsayawa takara a zaɓen 2023

Ya ce a matsayinsa na ɗan jiha mai kishi ya zama wajibi ya fito ya ba da gudummuwa don ceto jihar daga halin rashin tsaro.

Zamfara- Wani jigon APC a jihar Zamfara, Ɗakta Dauda Lawal, ya fice daga jam’iyya mai mulki ya koma PDP, kamar yadda Chennels tv ta rawaito.

Lawal, tsohon babban daraktan First Bank, ya kuma ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Zamfara ƙarƙashin inuwar sabuwar jam’iyyarsa PDP.

Ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi gaban dandazon masoya da magoya bayansa a gidansa da ke Gusau, babban birnin Zamfara.

Ɗan takarar gwamnan ya bayyana gwamnatin APC a matakin ƙasa da jiha da matsayin wacce ta gaza, inda ya ƙara da cewa jam’iyyar ta gaji kuma ta yi rauni.

Meyasa ya tsaya takara a PDP?

Dakta Lawal ya yi bayanin cewa ya yanke shawarar shiga tseren takarar gwamna ne saboda damuwarsa da tsaro da kuma kalubalen tattalin arziƙi da ya addabi Zamfara.

Ya ce jahar Zamfara ce kan gaba da matsalar tsaro ta fi yi wa katutu, bisa haka a matsayin ɗan jiha mai kishi akwai bukatar ya ba da gudummuwa wajen kawo canji a harkokin gwamnati.

A kalamansa ya ce:

“Kowanen mu ya na da masaniyar halin tsaron da muka fuskanta, a yau zan iya cewa jahar Zamfara na ɗaya daga cikin wurin da lamarin ya fi muni idan ma ba za’a iya cewa ita ce lamba ɗaya ba.”

“Kuma maganar gaskiya idan ba bu tsaro, rayuwa ba zata yi dadi da amfani ba kuma ba yadda muka iya.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here