Dalilin da Yasa na Ajiye Aikina – Jami’in Diflomasiyyar Rasha

 

Wani jami’in diflomasiyyar Rasha ya ajiye aikinsa saboda mamayar da ƙasar ke yi a Ukraine, yana mai cewa abu ne da bai dace ba.

Boris Bondarev, ya ajiye mukamin nea ofishin jakadancin kasar a Majalisar Dinkin Duniya da ke Geneva.

Ya ce bai taɓa jin kunyar Rasha ba kamar lokacin da ta tura dakarunta zuwa sassan iyakokin kasar ba.

Mr Bondarev, ya zargi ma’aikatar harkokin wajen Rasha da da yaɗa ƙarya da furta kalaman kiyayya.

A hirarsa da BBC, ya ce yana fatan matsayar tasa zata taimaka wajen gina sabuwar rayuwa anan gaba, sannan ya kuma bayyana fargaba akan tsaron lafiyarsa a yanzu

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here