Barcelona ta Bayyana Wanda Zai Maye Gurbin Lionel Messi

 

Ronald Koeman yana ganin Barcelona za ta kai labari duk da Lionel Messi ya tashi.

Kocin kungiyar ya ci buri a kan irinsu Antoine Griezmann su maye gurbin Tauraron.

Akwai lokacin da ake jita-jitar ba a shiri tsakanin Griezmann da Messi a Barcelona.

Barcelona – Kocin kungiyar Barcelona, Ronald Koeman, ya yi magana a kan yadda za su samu kansu bayan tauraron ‘dan wasan nan, Lionel Messi ya tashi.

Ronald Koeman ya na sa ran cewa za a samu wani wanda zai maye gurbin da Lionel Messi ya barci a cikin ‘yan wasan da suke buga wa kungiyar kwallon.

Gerard Pique ya bayyana cewa zuciyar ‘yan wasan Barcelona ya mutu a dalilin tashin Lionel Messi.

Metro ta rahoto cewa idanun Ronald Koeman suna kan ‘dan wasa gabansa, Antoine Griezmann wanda ya yi kwallo na shekaru biyu tare da Messi a kungiyar.

Rahoton yace amma duk da haka, mai horas da ‘yan wasan, Koeman yana ganin Antoine Griezmann zai iya bin sahun tsohon abokin aikinsa watau Messi.

Mu na da yara da sabbin ‘yan wasa – Koeman

“Duk da ban-kwana da aka yi da Leo Messi, muna shirya wa sabuwar kakar da za a shiga.”

“Da ‘yan wasanmu da ke nan, da cefanen da mu ka yi, mu na kuma da kanan ‘yan wasa masu tashi, wanda tun asali da su wannan kulob din ya dogara.” “Akwai bukatar ya zama mu na da ‘dan wasan da ya fi kowa, amma ka da mu canza salonmu, Griezmann ya buga wannan lambar, ya kuma tabuka.”

Kungiyar Barcelona babu Lionel Messi

Kamar yadda jaridar ta rahoto, Barcelona za ta gamu da kalubale a shekarar 2021/22 ganin cewa ta rabu da Messi wanda ya yi shekara da shekaru ya na tashe.

Bugu da kari, sabon ‘dan wasan Argentina, Sergio Aguero ba zai fara buga wasa ba sai nan da wasu ‘yan makonni, a sakamakon wani sabon rauni da ya samu.

Kungiyar ta gaza ba tauraron ‘dan wasan sabon kwantiragi ne saboda matsalar rashin kudi, hakan ta sa ya koma kungiyar Paris Saint-Germain a kasar Faransa

Akwai lokacin da tsohon dillalin, Griezmann, Eric Olhats yace Lionel Messi ya hana tsohon ‘dan wasan na Athletico Madrid sake wa, amma shi ya musanya hakan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here