‘Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Matar Tsohon Kansilan Jahar Zamfara, Babangida Ibrahim da Jaririnta

 

Wasu yan bindiga sun kutsa gidan tsohon Kansila da tsakar dare sun sace matarsa da kuma jaririnta ɗan wata 7.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:00 na dare ranar Laraba.

Kwamishinan yan sandan Zamfara, Hussaini Rabi’u, ya bada umarnin tsaurara bincike da kuma kamo maharan.

Zamfara – Rundunar yan sanda reshen jahar Zamfara tace wasu yan bindiga sun sace matar wani tsohon kansila, Babangida Ibrahim, da jaririnta ɗan wata 7, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin rundunar yan sandan jahar, SP Muhammad Shehu, ya shaidawa hukumar dillancin labarai NAN cewa:

“Maharan sun kai hari gidan tsohon kansilan dake Damba yankin Gusau, babban birnin Zamfara, da misalin karfe 12:00 na dare ranar Laraba.”

Ina Kansilan yake yayin harin

A cewar kakakin yan sandan jahar tsohon kansilan ya tsira da harbin bindiga a jikinsa kuma a halin yanzun ana bashi kulawa a asibiti.

Daily Nigerian ta ruwaito SP Shehu yace:

“Jami’an yan sanda na cigaba da gudanar da bincike da bibiyar yan bindigan domin kuɓutar da mutanen cikin koshin lafiya.”

Kwamishinan yan sanda ya bada umarnin tsaurara bincike

Bayan samun rahoton kai harin, Mr. Shehu yace kwamishinan yan sandan jihar Zamfara, Hussaini Rabi’u, ya bada umarnin binciko yan bindigan da kamo su.

Shehu yace:

“Kwamishinan yan sanda, CP Husaaini Rabi’u, ya bada umarnin gaggawa na gudanar da binciken kwakwaf kan lamarin da kamo waɗanda suka kai harin.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here