Muhimmanci Zaɓen Gwamnonin Jihohi a Najeriya

 

Makonni bayan zaɓen shugaban ƙasa, al’ummar Najeriya na gudanar da zaɓen gwamnonin jihohi 28 na faɗin ƙasar.

Akwai kimanin ƴan takara 400 da ke takarar gwamna a jihohin daban-daban na Najeriya.

Jiha wani mataki ne na gwamnati a Najeriya, baya ga matakin tarayya da na ƙananan hukumomi.

Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa ke lura da harkokin tsaron ƙasa, da harkokin ƙasashen waje da kuma tattalin arziƙi.

Yayin da su kuma gwamnoni suke kula da harkokin jihohinsu.

Sukan samar da hanyoyi da makarantu da kuma kiwon lafiya.

Tasirin gwamnoni a siyasar Najeriya?

Gwamnoni suna da matuƙar ƙarfin faɗa a ji a lamurran Najeriya.

Haka nan gwamnoni ne ke sarrafa maƙudan kuɗaɗen da kasafin kuɗin jihohinsu suka ƙunsa.

Cin zaɓen gwamna lamari ne da ke iya sauya rayuwar ɗan siyasa ta hanyar ƙarfafa tasirin da yake da shi.

Wasu daga cikin gwamnoni kan share hanyarsu ta zama sanatoci bayan kammala mulkin jihohinsu.

Mene ne mutane za su yi la’akari da su?
Abubuwan da mutane za su yi la’akari da su wajen zaɓen gwamnoni sun banbanta daga wata jiha zuwa wata.

Misali, matsalar cunkoson ababen hawa da ta muhalli da hanyoyin sufuri su ne manyan matsalolin da ke addabar jihar Legas.

Jihohi irin su Kaduna, da Katsina da Zamfara kuwa na fama da matsalar tsaro.

Akwai kuma jihohi irin Kano da Sokoto, da Bauchi waɗanda ke fama da matsalar daba.

Sannan akasarin jihohin ƙasar na fama da yawaitar mutane da ke fama cikin ƙangin talauci

A jihar Adamawa zaɓen ya ɗauki sabon salo, inda a karon farko cikin tarihi ake da ƴar takarar gwamna mace, a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar.

Wannan wani muhimmin mataki ne a siyasar ƙasar, wadda mata ke a sahun baya wajen yin takara a muhimman muƙamai.

Akwai yiwuwar wannan mataki zai ƙara wa mata azama wajen takarar manyan muƙamai a ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here