Sayen ƙuri’a’: NDLEA ta Kama Wakilan Jam’iyya da Katunan Cirar Kuɗi
Jami’an hukumar yaƙi da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wasu mutum huɗu da ɗaruruwan katunan cirar kuɗi domin sayen ƙuri’a a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce an loda wa kowanne kati naira 10,000, tare da saka masa lambobin sirri, waɗanda ake zargin na sayen ƙuri’a ne.