Jami’an Hukumar EFCC Sun Dira a Ibadan

Jami’an hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-ƙasa, EFCC sun je rumfar zaɓe mai lamba 11, a birnin Ibadan na jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Rumfar zaɓen dai ita ce rumfar da gwamnan jihar Seyi Makinde zai kaɗa ƙuri’arsa.

Jami’an na EFCC dai kan ziyarci rumfunan zaɓe domin hana sayen ƙuri’a, da aikata sauran laifukan da suka shafi almundahana a rumfunan zaɓen.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here