Dakarun NAF Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 23 Yayin Yukurin Satar Shanu da Kona Gidaje
Rundunar sojin Najeriya, wacce ta kunsa sojin saman NAF uku da jiragen yaki sun tarwatsa a kalla sansanin ‘yan ta’addan bakwai a jihar Kaduna a ranar Laraba.
Haka zalika, an gano yadda dakarun suka sheke ‘yan bindiga 23 yayin da suka yi yunkurin sace shanu 200 gami da kona gidaje a yankin Danya na jihar Zamfara.
Har ila yau, dakarun sun halaka a kalla wasu 17 da ake zargin ‘yan ta’adda ne gami da tarwatsa baburansu da kwale-kwale a jihar Neja bayan tabbatar da hatsabibai ne.
Dakarun sojin saman Najeriya sun budewa tawaga biyu ta masu satar shanu yayin da suka kai wani samame a Jihar Zamfara da Neja wuta ta jiagen yaki.
Read Also:
Haka zalika, dakarun, tare da soji uku na saman Najeriya (NAF), jiragen yaki da jiragen bindigu sun kai samame ga ‘yan ta’addan a jihar Kaduna gami da tarwatsa sansanin su a ranar Laraba.
Wani jami’in binciken sirri na sojin, wanda ke daya daga cikin wadanda suka kai samamen Zamfara, ya bayyana yadda aka sheke ‘yan ta’adda 20 a wurin Kofar Danya na jihar, yayin da suka yi yunkurin sace shanu 200.
Majiyar ta bayyana yadda, “Ba tare da bata lokaci ba, biyu daga cikin mayakan jirgin saman NAF suka yi dirar mikiya a tsakiyar tawagar ‘yan ta’addan gami da bude musu wuta yayin da suka yi yunkurin sace shanu 200 a Kofar Danya na jihar zamfara.
“A lokacin da suka isa wurin, tawagar sun hango ‘yan ta’addan masu tarin yawa kan babura, suna kokarin shiga kauyuka gami da sace shanu.
“Ba tare da zato ko tsammani ba, jiragen yakin suka budewa ‘yan ta’addan wuta tare da dasa abubuwa masu fashewa, gami da halaka ‘yan ta’adda 23 bayan wadanda suka samu raunuka.”