Bayan Biyan Kudin Fansa: An Saki ‘Yan Kasuwan da Aka Sace a Hanyar Zuwa Daurin Aure a Zamfara

 

Mutanen nan da aka dauke a hanyar zuwa daurin aure a Zamfara sun samu ‘yanci a makon nan.

Sakataren kungiyar ‘yan kasuwan waya na Bebeji ya tabbatar da cewa an saki abokan aikin na su.

A karshe ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da su, sun nemi a biya N400, 000 a kan kowane mutum.

Zamfara – Mutum 29 da aka dauke a hanyar zuwa wani daurin aure a jihar Zamfara sun samu ‘yanci bayan kwana da kwanaki a hannun ‘yan bindiga.

A jiya wani wanda yake kusa da wadanda aka dauka, ya shaidawa gidan talabijin na Channels TV cewa wadannan Bayin Allah sun bar hannun ‘yan bindiga.

Ashiru Zurmi wanda Sakataren kungiyar ‘yan kasuwan waya ne ya shaidawa manema labarai cewa abokan aikin na sa sun samu ‘yanci, za su koma gidajensu.

A lokacin da aka zanta da shi, ya ce matasan da aka dauke su na hnayar su ta zuwa garin Gusau.

Su na hanyar zuwa Gusau

“Mutanenmu sun samu ‘yanci a yau, ina mai tabbatar maku da wannan. Yanzu haka su na kan hanyar zuwa garin Gusau.” – Majiya

A hirar da aka yi da shi, Zurmi bai bayyana adadin kudin da ‘yan kungiyarsa ko ‘yanuwan wadannan Bayin Allah suka biya a matsayin kudin fansa ba.

An ce kowa ya biya N400, 000

Majiyar ta iya fadawa gidan talabijin cewa wadannan mahalarta daurin aure sun fito ne kurum. Premium Times ta ce sai da aka hadawa ‘yan bindigan kudi.

Abdullahi Lawal wanda ‘danuwansa na cikin wadanda aka dauke, ya ce sai da ‘yanuwa suka tara N330, 000, sannan abokan aikinsa suka tattaro ragowar kudin.

cewar Lawal, ‘yan bindigan sun bukaci kowane dangi su tanadi N400, 000. Wasu sun iya hada wannan kudi, su dai ba su iya hada duk abin da aka nema ba.

‘Yan kasuwan sun shafe kwanaki kimanin 13 su na hannun ‘yan bindiga a jeji, tun bayan da aka tare su a kauyen Dogon Awo da ke tsakanin Tureta da Bakura.

A lokacin an bukaci a biya Naira miliyan 145 kafin a fito da su. Gwamnatin Zamfara ta yi alkawarin za ta yi bakin kokarinta na ganin an ceto mutanen.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here