Ba Laifi ba ne, Damukaradiyya Ake yi, mu ba Fada mu ke yi da Ahmad Lawan ko Wani ba- Bashir Machina

Bashir Sheriff Machina ya sake maida martani bayan hirar da aka yi da Sanata Abdullahi Adamu.

An ji shugaban na Jam’iyyar APC yana kare matsayar APC na mikawa INEC sunan Ahmad Lawan.

Hon. Machina ya karyata shugaban APC na kasa, ya ce sam Lawan bai nemi takara a jihar Yobe ba.

Yobe – Hon. Bashir Sheriff Machina ya fito ya yi martani ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu a kan wasu kalamai da ya yi.

Da yake zantawa da BBC Hausa a ranar Juma’a, 24 ga watan Yuni 2022, Bashir Sheriff Machina ya yi Allah-wadai da irin maganganun Abdullahi Adamu.

Kamar yadda ya fada, ‘dan takaran na Sanatan Yobe ta Arewa ya ce yana neman hakkinsa ne a APC, domin bai fada da Sanata Ahmad Lawan ko wani.

Machina ya fadawa BBC cewa bai dace dattijo irin Sanata Abdullahi Adamu ya rika fadar maganganu masu zafi a kan shi ba, a lokacin shirin zabe.

Kalamansa ba su dace ba

“Dattijo bai kamata ya yi magana irin wannan a daidai wannan lokaci ba. Idan aka sako zabe a gaba, bai a yin kalmomi masu zafi ko batanci ko barazana ga mai neman ‘yancinsa.

Ba laifi ba ne, damukaradiyya ake yi, mu ba fada mu ke yi da Ahmad Lawan ko wani ba. Ba mu fada da kowa.” – Bashir Machina.

Mun tsaya a matsayinmu na masu neman hakkinmu. Bai dace babban mutum ya fito karara, yana irin wannan kalma ba.”

‘Dan siyasar yace su na gudun shugaban na APC ya rika yin katsalandan, don haka ya gargade shi da cewa ya guji tsoma masu baki a siyasar jihar Yobe.

Me ya yi zafi?

A cewarsa, Ahmad Lawan da aka mikawa INEC sunansa, sam bai cikin ‘yan takaran APC a zaben. Machina ya ce kage ne a ce shugaban majalisa ya shiga zabe.

Tsohon ‘dan majalisar ya ce su na da sakamakon zabe, kuma duk wani ‘dan Najeriya ya ga sakamakon zaben da aka fitar cewa Lawan bai yi takara ba.

“Duk wani mai hankali ya san ranar da aka kebe na wannan zaben tsaida gwani. Kuma kowa ya san an je anwatar da wannan zabe.” – Bashir Machina.

Bugu da kari, Hon. Machina ya ce ya kamata Sanata Adamu ya tsaya a matsayinsa na shugaban APC na kasa, ba shugaban wata kabila ko wanni bangare ba.

A karshe, Bashir Machina ya bukaci tsohon gwamnan na jihar Nasarawa da ya guji jagwalgwala jam’iyyar APC ta jihar Yobe, sannan ya nemi afuwarsa a fili.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here