Nigeria za ta Kai wa Chadi Wutar Lantarki

Gwamnatin Nigeria ta shirya tsaf domin fara aikawa Chadi wutar lantarki, duk da cewa da ma can tana aikawa jamhuriyar Niger, Benin da Togo.
A halin yanzu, cibiyoyi 27 bakwai ne ke rarraba wutar lantarki a Nigeria, yayin da 11 ba sa aiki, kuma karfin wutar ya sauko zuwa 3,474.5MW – Sai dai duk da wadannan matsaloli da kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa TCN ke fuskanta, ya ce Nigeria na da karfin aikawa Chadi wutar Gwamnatin tarayya na duba yiyuwar kai wa jamhuriyar Chadi wutar lantarki, biyo bayan bukatar hakan da makwabciyar kasar ta gabatar. Kamfanin rarraba wutar lantarki mallakin gwamnati ya bayyana hakan a ranar Lahadi a taron da aka gudanar makon da ya gabata don duba yiyuwar kai wa Chadi wutar lantarki. A halin yanzu Nigeria na da karfin wuta tsakanin 3,000MW zuwa 4,500MW, kuma ko a yanzu, Nigeria na kai wutar lantarki ga jamhuriyyar Niger, Benin da Togo
A ranar Lahadi, karfin lantarkin ya sauko daga 3,474.5MW daga 3,776.5MW da ya ke a ranar Asabar, a cewar rahoton sashen kula da lantarkin Nigeria NESO. Adadin cibiyoyin wutar kasar da ba sa samar da wutar lantarki sun haura zuwa 11 da misalin karfe 6 na safiyar Lahadi, daga 8 da ake da su a ranar Asabar.
Cibiyoyin da suka daina aiki, su ne; Geregu II, Sapele II, Alaoji, Olorunsogo II, Omotosho II, Ihovbor, Gbarain, Ibom Power, AES, ASCO da Trans-Amadi. A halin yanzu, cibiyoyi 27 bakwai ne ke rarraba wutar lantarki a kasar, kuma suna karkashin kulawar kamfanin TCN.     A ranar 22 ga watan Yunin 2020 ne kamfanin TCN ya sanar da cewa gwamnatin Chadi ta bukaci gwamnatin Nigeria da ta dunga kai mata wutar Lantarki don saukaka matsalar lantar da suke yi. Ya bayyana cewa jakan Chadi a Nigeria, Mr Abakar Chachaimi, ya gabatar da bukatar a lokacin da ya jagoranci tawaga zuwa ga ministan makamashi, Mr Sale Mamman, a Abuja.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here