Jami’an NSCDC sun Kama Mutane 10 Bisa Zargin Fasa Bututun Man Fetur

 

Hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC, reshen jihar Ribas, ta ce ta kama mutum 10 bisa zargin fasa bututun man fetur, da satar ɗanyen mai da kuma safarar haramtattun abubuwa.

Cikin saƙon da hukumar ta wallafa a shafinta na X wanda a baya ake kira Tuwita, ta ce ta kama wasu motoci guda tara maƙare da kayan sata a cikin buhunhuna, tare da lita 28,225 ta man dizel.

Mutum goman da ake zargin sun haɗar da, Chinedu Michael wanda aka bayar da belinsa watanni biyu a baya, lokacin da hukumar ta kama shi bisa zargin tace man fetur ba bisa ƙa’ida ba.

Da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke Fatakwal, babban birnin jihar Ribas, Kwamandan jihar, Basil Igwebueze ya bayyana cewa, rundunar ta cafke wadanda ake zargin ne a wurare daban-daban a fadin jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com