Dakarun Soji Sun Halaka ‘Yan Ta’adda a Dajin Sambisa da ke Jihar Borno

 

Jami’an rundunar sojin Operation Haɗin Kai sun halaka ‘yan ta’adda da dama a wani samame da suka kai dajin Sambisa.

Kakakin hukumar sojin sama ya bayyama cewa sojojin sun yi wa yan ta’addan ruwan wuta ta sama bayan samun bayanan sirri.

A cewarsa, bayan harin sun gano cewa samamen ya sheƙe su da yawa kana ya tarwatsa sansaninsu a Suwa.

Borno – Dakarun sojin saman Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai da ke Arewa maso Gabas sun tarwatsa ragowar ‘yan ta’addan da suka hana zaman lafiya a yankin dajin Sambisa na jihar Borno.

Gwarazan sojojin sun samu wannan gagarumin nasara ne biyo bayan luguden bama-baman da suka yi kan mafakar ‘yan ta’addan a garin Suwa, ƙaramar hukumar Kala Balge.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa samamen, wanda jiragen sojin saman suka kai da sanyin safiyar ranar Litinin, ya halaka tulin mayaƙan ƙungiyar ‘yan ta’adda a dajin.

Yadda sojoji suka tarwatsa ‘yan ta’adda a Sambisa

Kakakin hukumar sojin saman Najeriya, Edward Gabkwet, ya shaida wa ‘yan jarida a Abuja ranar Talata cewa an kai wannan farmaki ne bayan tattara bayanan sirri.

Ya ce bayanan sirrin da sojojin suka samu ya nuna cewa ‘yan ta’addan na ƙulle-kulle kai sabon mummunan harin kan mutane.

Ya ce bayanan da aka samu sun kuma nuna cewa kungiyar ta ‘yan ta’addan ta kammala shirin kai hari kan sansanin sojoji da ke Rann a karamar hukumar Kalabalge ta jihar Borno.

A cewarsa, nan take aka tura sojoji suka kai hari ta sama kuma bayan gudanar da bincike an gano cewa ruwan wutan ya halaka yan ta’adda da dama tare da lalata maɓoyarsu.

Haka zalika, wannan nasara ta gurgunta ƙarfin ‘yan ta’addan ta yadda ba zasu iya kai hari kan jami’an tsaro ko fararen hula ba, kamar yadda The Cable ta tattaro.

“A kokarin kakkabe ragowar ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas da tsaftace shiyyar daga ayyukan ta’addanci, dakarun sojin saman Operation Hadin Kai sun kai hari Suwa karamar hukumar Kala Balge a Borno ranar 11 ga Satumba.”

“Idan dai za a iya tunawa, garin Suwa ya kasance tungar ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin Gezuwa kusa da dajin Sambisa har sai da sojoji da sauran jami’an tsaro suka fatattake su.”

– Edward Gabkwet

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com