Gwamna Ortom ya Caccaki APC Kan Yadda Tsofaffi Suke Shirin Tsayawa Takara a Jam’iyyar
Gwamna Samuel Ortom na Jihar Binuwai ya shawarci ‘yan Najeriyan da suka zarce shekaru 70 da haihuwa da su hakura da takarar shugaban kasa.
Kamar yadda ya ce, ya kamata su bai wa masu jin a jika da ilimin zamani wuri don su amshi ragamar shugabancin kasa.
Gwamnan ya yi maganar ne jiya yayin da Bukola Saraki, Bala Mohammed da Tambuwal suka kai masa ziyara don jin matakan da PDP ta dauka na tsayar da dan takara.
Jihar Benue – Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom ya ba ‘yan Najeriya da suka wuce shekaru 70 shawarar dakatawa daga tsayawa takarar shugaban kasa.
A cewarsa, zai fi dacewa su ba wa masu kananun shekaru da kuma ilimi irin na zamani damar shugabanci, Vanguard ta ruwaito.
A jiya, gwamnan ya yi wannan bayanin ne yayin da ya amshi tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto da Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi, wadanda suka je tuntubarsa don sanin shirin jam’iyyar PDP na tsayar da dan takara.
Read Also:
Ya caccaki APC saboda yadda tsofaffi suke shirin tsayawa takara a jam’iyyar
Kamar yadda Vanguard ta nuna, gwamnan ya ce:
“Ina so in shawarci ‘yan Najeriya dangane da hadin kai. Sanin kowa ne cewa a baya an samu tarin nasarori saboda dunkulewar ‘yan Najeriya wuri guda. Suna kai ziyara har ga ‘yan uwansu na kudu yayin da suke nuna burinsu na tsayawa takara. Ya kamata mu yi aiki tare. Duk da PDP jam’iyyar adawa ce, amma muna da dokokinmu.
“Shiyasa yanzu haka PDP a shirye take da ta ceto Najeriya ta kuma kara gina ta. Yanzu ku duba mutane ukun nan, a jiya (ranar Lahadi), akwai wani mutumin kirki daga Jihar Ribas, Gwamna Wike, wanda ya zo nan Jihar Binuwai yana neman tsayawa takarar shugaban kasa.
“Ku kalli wadannan matasan, ku hada su da tsofaffin can na APC da take son su tsaya takarar shugaban kasa a zamanin nan da ake ciki. Ya kamata a ba matasa dama. Ba zan kira suna ba, amma duk wanda ya wuce shekaru 70 kuma yake son ya tsaya takara, ba ya yiwa Najeriya fatan alheri.”
Yayin jawabi, tsohon shugaban majalisar dattawa, Saraki ya ce ya zo Jihar Binuwai ne don su tattauna sannan su san shirin da PDP take yi na tsayar da dan takarar shugaban kasa.