An Harbi Tsohon Mataimakin Gwamnan Zamfara, Ibrahim Wakkala a Harin Jirgin Kasar Abuja-Kaduna

Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara, Ibrahim Wakkala, na a cikin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja da aka kaiwa hari a ranar Litinin.

Wakkala ya samu rauni ta sanadiyar harbin bindiga bayan tawagar tsaro sun ceto shi daga hannun yan bindigar da suka yi garkuwa da shi a yayin harin.

Yana a hanyarsa ta dawowa ne daga babban taron gangamin APC da aka yi a karshen mako.

Kaduna- Tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Wakkala, ya ji rauni daga harbin bindiga a harin ta’addanci da aka kai kan jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja a ranar Litinin, 28 ga watan Maris.

Yan bindiga sun far ma jirgin kasan da ke dauke da daruruwan fasinjoji a tsakanin Katari da Rijana a jihar Kaduna.

Wani hadimin tsohon mataimakin gwamnan ya fada ma talbijin din Channel cewa an harbi Mista Wakkala ne wanda ke dawowa daga babban taron APC da aka yi a ranar Asabar a yayin musayar wuta tsakanin yan ta’addan da sojoji.

Ya kuma ce an kwashe shi zuwa wani asibitin sojoji da ke Kaduna domin jinya.

Kakakin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara, Yusuf Idris ya kuma tabbatar da lamarin ga gidan talbijin din.

Idris ya ce da farko yan bindiga sun sace tsohon mataimakin gwamnan a yayin harin amma sai tawagar hadin gwiwa ta DSS da sojoji suka yi nasarar ceto shi.

“Da farko sun sace shi amma sai DSS da sojoji suka ceto shi, a cikin haka ne ya ji rauni ta sanadiyar harbin bindiga a kafarsa.

“Ya daidaita sosai a yanzu, yana samun kulawar likitoci a asibitin jihar Kaduna.”

Daily Trust takuma nakalto Idris na kara cewa:

“Yana samun sauki sosai. Yana amsa kiraye-kirayen waya a gadonsa na asibiti. Na yi magana da shi kuma wasu mutane da dama ma sun yi. Babu wani abun tashin hankali.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here