Zaɓen Gwamna: Osinbajo Tare da Matarsa Sun Kaɗa ƙuri’unsu
Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo tare da mai ɗakinsa Mrs. Dolapo Osinbajo sun kaɗa ƙuri’unsu.
Mataimakin shugaban kasar tare da matarsa sun kaɗa ƙuri’un ne a zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihohi da ake gudanarwa a jihohin ƙasar.
Mista Osinbajo tare da Mrs Dolapo sun kaɗa ƙuri’un ne a ƙaramar hukumar Ikenne ta jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.