Paul Pogba: Abin da Ban Haushi, Ban Tube Takalmana ba
‘Dan kwallon Man United, Paul Pogba ya ce bai yi ritaya a kasarsa ba.
Read Also:
Ana rade-radin cewa ‘Dan kwallon zai daina buga wa kasar Faransa – Pogba ya zai kai ‘Yan jarida kotu a kan wannan labari na soki-burutsu ‘Dan wasan tsakiyan kungiyar Manchester United, Paul Pogba ya fitar da jama’a daga duhu a kan rade-radin da ake yi cewa ya ajiye kwallo a gida.
“Ba za ta sabu ba.” ‘Dan wasan mai shekara 27 a Duniya ya rubuta a shafinsa na Twitter jiya.
Pogba ya karyata wannan labari a dandalin sada zumunta, ya kira rahoton da labarin bogi, kunshe da hoton kanun wannan labari da ke yawo. “To …. (Jarida) ta sake yin abin da ta yi kenan. Shakka babu 100% na labarin bogi maras tushe, a je ana fadin abin da ban fada ba, kuma ban yi tunani ba.” ‘Dan wasan ya koka da yadda ake amfani da shi da kungiyar kwallon Faransa wajen karya. “Ina bakin ciki, fushi da mamakin yadda wasu ‘gidajen yada labarai; za su yi amfani da ni, su buga labaran karya a lamarin da ya shafi halin kasar Faransa.
“Ba na goyon bayan duk wani irin ta’addanci da tada rikici. Abin takaici wasu gidajen jaridu ba su yin abin da ya dace wajen buga labarai.” Inji Paul Pogba. Pogba ya yi barazanar shiga kotu da wadanda su ka buga wannan labari ba tare da tantance wa ba.