Jahar Plateau ta Sausauta Dokar Hana Fita a Jahar

 

Gwamnan jahar Filato ya sassauta dokar hana fita a wasu yankunan jahar bayan kwanaki.

A bayan an sanya dokar hana fita a wasu sassa uku na jahar Filato bayan barkewar rikici.

Gwamnan ya lissafo yadda sassaucin dokar hana fitan za ta kasance a yankunan uku.

Plateau – Gwamnatin jahar Filato ta sassauta dokar hana fita da aka kafa a kananan hukumomin Jos ta Arewa, Jos ta Kudu da Bassa, inji Daily Trust.

Gwamna Simon Lalong ya sanya dokar hana fita ne bayan tashin hankalin da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dama, kona gidaje da barnata dukiyar al’umma.

An kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a yankin Jos ta Arewa (inda aka fi samun tashin hankali), yayin da Jos ta Kudu da Bassa aka sanya dokar daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.

Dokar hana fitan ta kasance tana aiki har zuwa safiyar yau Litinin 30 ga watan Agusta lokacin da gwamnan jahar ya sake sassauta ta.

Lalong ya ce an sassauta dokar hana fita a Jos ta Arewa daga awanni 24 zuwa daga 6 na yamma zuwa 6 na safe, yayin da a Bassa da Jos ta Kudu wanda tun farko karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe yanzu zai kasance daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Batun zirga-zirga a yankunan

“Dokar hana yawo da a daidaita sahu (Keke NAPEP) da masu talla za ta ci gaba da aiki a cikin garin Jos/Bukuru, kuma taron tattalin arziki da saka hannun jari na Filato da aka shirya yi a ranar 1 da 2 ga Satumba 2021 an dage ranarsa. Za a sanar da sabon kwanan wata da kuma sanar da duk masu gayyatar mu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here