Rashin Mahajjata Daga Kasashen Duniya: Asarar da Kasar Saudiyya ta Tafka

Saudiyya na daga cikin manyan kasashen duniya da annobar cutar korona ta haifar da koma baya gahanyoyin samun kudaden shigarta.

Saudiyya na samum ɗumbin kudaden shiga a lokutan ayyukan Hajji da Umara da miliyoyin Musulmai kan halarta a duk shekara daga kasashen duniya.

Kamar dai a shekarar bara, bana ma haka batun yake game da rage adadin wadanda za su halarci aikin hajjin, duk da cewa yawan ya ɗara na bara din.

Rashin zuwan mahajjata ƙasar daga ƙasashen duniya na nufin rage yawan kuɗaɗen shigar Saudiyya a fannoni da dama da suka haɗa da na sufuri da na otel-otel har ma fannin abinci da sauran kayayyaki.

A wannan maƙalar, BBC Hausa ta yi nazari kan irin asarar da rashin zuwan mahajjatan ƙasashen duniya ke jawo mata.

BBC ta tattauna da tsohon shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya, kuma masani kan harkokin da suka shafi ayyukan hajjin, Barista Abdullahi Mukhtar.

Masanin ya ce baya ga man fetur, babu wani abu da ke bai wa al’umma da kuma gwamnatin Saudiyya kuɗin shiga kamar ayyukan Hajji da Umara.

Ya kuma ƙara da cewa a ƙiyasin shekara ta 2019, wanda shi ne hajjin da aka samu mahajjata da dama daga kasashen duniya kafin annobar cutar korona, Saudiyya ta samu kudin shiga dala biliyan 12.

”Wato wannan ƙididdiga ce kawai ta gwamnati da ke rubuce, wacce ba a hada da abubuwan da watakila ba a sanya su a littafi ba kamar masu ƙananan sana’o’i ba,” in ji shi.

”To duk wadannan idan aka ce babu aikin hajji, kuma an shekara ba a yi Umara ba yadda aka saba yi, asara ce mai yawan gaske ga ita kanta gwamnati da kuma al’umma da suke amfana daga aikin ibada da mutane ke zuwa yi”.

Ta ɓangaren ƴan kasa wace irin asara suka tafka?

Ko shakka babu dai ayyukan hajji da Umra in ji masanin kan harkokin ayyukan hajji da umarar Abdullahi Mukhtar na bai wa mutane da daman gaske damar samun kudin shiga, in ji masanin.

Ya ƙara yin misali da aikin hajjin da aka yi a shekara ta 2019.

”An yi amfani da motocin safa-safa masu yawa domin jigilar alhazan a lokacin aikin hajjin shekaarar 2019, da kuma yadda aka samu koma baya mai yawan gaske bayan barkewar annobar korona,” in ji shi.

Ya kuma kara da cewa, an yi amfani da akalla motoci 32,978 a Aikin Hajjin shekarar 2019.

”Yanzu ko da direba ne kawai za a dauka mutum 32,000 a ce shekara ta zagayo wadannan mutane ba su samu aikin yi ba, ai ba karamar asara bace, ballantana kowace mota tana da mai rakiya da ake kira kwandasta,” ya ce.

Ma’aikatar ƙididdiga ta Saudiyyaa ta nuna cewa a hukumance ma’aikata da suke fitowa su yi aiki sun kai mutum 350,830 in ji Barista Mukhtar.

”Adadin wadannan mutane suke yi wa alhazai hidima mutum miliyan biyu da dubu hudu da suka je aikin hajjin wannan shekarar,” in ji shi.

”To wadannan mutane akasarinsu ba su samu aikin yi ba a cikin shekaru biyu, don haka hakika asarar na da yawan gaske.

“Kuma wannan misali kadan ne daga ciki, ba a hada da misali da maganar ma’aikatan jirgi, da batun tashi da saukarsa, da sauran abubuwa da daman gaske ba.”

“Mutum miliyan 2.4 daga kasashen waje, da mutum 600,000 ‘yan ƙasa da suka fito Aikin Hajji, wannan fa bai hada da ma’aikata da ake zuwa da su daga kasashe domin taimaka wa mahajjatansu ba, na cikin gida ne kawai,” a cewar Alhaji Abdullahi.

Ya ƙara da cewa rashin aikin nan shi zai sanya waɗannan ma’aikatan kusan kashi 80 bisa 100 daga cikinsu ba su samu aikin yi ba.

Wasu daga cikin masu ƙananan sana’o’i da wadanda da suka rasa aikin yi
Masu gidajen haya
Masu shaguna
Masu jiran shaguna
Masu share-share
Ƴan dakon kaya
Ƴan kabu-kabu
Masu kasa kaya
Masu yi wa alhazai hidimoimi da gwamnai ke dauka
Masu lura da gidajen haya
Ma’iakata masu zuwa daga kasashe domin taimaka wa alhazansu
Ma’ikata masu lura da tashi da saukar jiragen sama da fasinjoji
Direbobin kamfanonin manyan motocin safa-safa, da sauransu.

Asarorin a bangaren gwamnati

Ko shakka babu Saudiyya ta tafka manyan asarori sakamakon dakatar da masu zuwa yin aikin hajjin daga kasashen duniya, da kuma taƙaita yawan ƴan kasar da za su halarci aikin hajjin.

Kamar yadda Alhaji Abdullahi Mukhtar ya bayyana cewa girman Aikin Hajji ga gwamnatin Saudiyya da kuma al’ummar Musulman duniya za a iya ƙiyasta su ta bangaren kudi.

“Amma abu ne wanda yake zamani ya zo da dole lissafin tattalin arziki na kowace kasa da mai shiga da kuma mai fita ana duba shi ta wasu fuskoki da ake ɗora su a kan mizani na tattali arziki na kasa.

”Babu shakka rashin yin Aikin Hajji ga Saudiyya da su kansu baƙi masu shiga ya jawo manyan asarori wa gwamnati da kuma ‘yan kasa.

“Saboda irin ɗumbin kudaden da ƙasar ta saba samu a irin wannan lokaci,” ya ce.

Aikin hajji na shekarar 2019 in ji masanin, ya samar wa da gwamnatin Saudiyya kuɗaɗen shiga dala biliyan 12, kana kusan kaso 20 daga tattalin arzikin da ake samu daga abin da bai shafi mai ba.

“Idan kuma aka ƙididdige gaba daya tattalin arzkin Saudiyya a wannan shekarar za a iya cewa ya kawo musu kusan kashi bakwai zuwa 12.

“Don haka ba ƙaramin koma baya da kuma tafka asara Saudiyya ta yi sakamakon annobar cutar korona da ta haifar da haramta wa miliyoyin Musulmai halartar aikin hajjin da suka saba zuwa a duk shekara ba,” in ji shi.

Lafiya da kwanciyar hankalin mahajjata fiye da kuɗin shiga

Abin da Abdullahi Mukhtar ya ƙara shaida wa BBC game da yadda al’amura za su kasance shi ne ita Saudiyya Allah ya hore mata ƙarfin tattalin arziki da kuma ma’aikata masu hangen nesa.

Yana ganin babu shakka za su fito da hanyoyi da dama na tallafa wa ƙasarsu domin ganin cewa sun rage musu raɗaɗin wannan asarar da suka yi.

“Na yi imanin za ta ɓullo da wasu hanyoyin da za su samar wa da mutanenta ayyukan yi.

“Kamar yanzu misali hajjin bana na shekarar 2021 an yarda mutum 60,000 su fita su yi Aikin Hajjin.

“Wannan ƙari aka samu a kan na bara, don haka adadin mutane da aka ɗauka sun ƙaru a kan na bara.

“Don haka da yardar Allah a shekara mai zuwa ta 2022 adadin wadanda za su je aikin hajjin zai ƙaru, sai dai zai dauki lokaci kafin a ce an koma yadda ake yi a baya da miliyoyin mutane ke zuwa,” a cewarsa.

Ya kuma bayyana cewa Saudiyya za ta yi kyakkawan nazarin yadda aikin zai kasance a dogon zango da kuma yadda ‘yan kasar za su samu wadata.

Amma kuma duk da girman wannan matsala da asarori da ake magana a kai in ji masanin, ita Saudiyya ta fi bayar da muhimmanci ga a yi Aikin Hajji lafiya fiye da saun kuɗin shiga.

“Darajar mahajjaci daya, ya shiga ya yi Aikin Hajjinsa cikin aminci, da kwanciyar hankali da kyakkyawan tsaro da kuma lafiya, ya fi mata muhimmanci fiye da abin da za ta samu.

“Don haka suna ƙoƙarin tabbatar da ganin cewa Aikin Hajji bai zama wani wuri na yaɗa cuta ba saboda mutanen da ke zuwa daga sassa daban-daban na duniya” a cewarsa.

Annobar cutar Corona ta haifar da manyan matsalolin koma bayan tattalin arziki a kasashen duniya.

Baya ga hakan ta kuma haifar da karin matsaloli na rashin aikin yi musamman a tsakanin matasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here