Ya Kamata Mutane su Saba da Tsadar Kayan Masarufi – Miguel Patricio
Shugaban daya daga cikin manyan kamfanonin samar da kayan abinci na duniya na Kraft Heinz, ya ce ya kamata mutane su saba da tsadar kayan masarufi.
Read Also:
Miguel Patricio ya shaida wa BBC cewa matsin tallatin arziki da hauhawar farashin kayayyaki da kasashe ke fuskanta sakamakon barkewar annobar cutar corona na daga cikin dalilan da lamarin ya yi kamari.
Ya kara da cewa kamfaninsa ya fuskanci tashin farashin kayayyakin da yake amfani da su wajen sarrafa kayan abinci, don haka dole abokan hulda su ma su fuskanci karin farashi.
Amma ya ce fasahar zamani da sabon irin da ake da su ka iya taimaka wa manoma su kara samun amfanin gona mai kyau.
Hukumar farashin kayan abinci ta majalisar Dinkin Duniya ta ce an fuskanci tashin farashin da ba a taba gani ba cikin shekaru 10.