Yaduwar Korona: Akwai yiwuwar Saka Sabon Takunkumi kwanan nan a Najeriya – PTF

Alamu na nuna za a iya maka sabon takunkumi kwanan nan a Najeriya.

Kwamitin PTF ya ce ‘Yan Najeriya ba su bin sharudan da aka gindaya.

Kwamitin ya ce za a rufe gari idan har Coronavirus ta na yaduwa sosai.

Alamu su na nuna cewa za a iya sake garkama takunkumi nan ba da dadewa ba a Najeriya saboda karuwar masu dauke da COVID-19.

Kwamitin da shugaban kasa ya kafa na PTF mai yaki da annobar COVID-19, ya ce mutane ba su bin ka’idoji don haka cutar ta ke ta yaduwa.

Daga cikin matakan da kwamitin zai iya dauka domin ganin an dakile yaduwar wannan cuta ta COVID-19, The Nation ta ce har da rufe gari.

Shugaban kwamitin, Dr. Sani Aliyu, ya bayyana cewa muddin aka cigaba da samun karin masu kamuwa da cutar, watakila a maka takunkumi.

Da yake magana, Dr. Sani Aliyu, ya ce ta haka ne kurum za a iya shawo kan wannan annobar.

Jaridar ta rahoto Dr. Aliyu ya na cewa: “Idan alkaluma su na tashi, adadin masu cutar ya na yin sama, za mu duba duk matakan da mu ke dasu.”

“Watakila ba za su yi mana dadi ba, abin ba zai kai garkame gari wahala ba” inji kwamitin na PTF.

Shugaban kwamitin ya ke cewa mutane 33 sun mutu a makon da ya gabata a sakamakon COVID-19. “Mu na cewa duk sun mutu a banza kenan?”

“Mun samu mutane 6, 000 dauke da cutar a cikin makon nan da ya wuce. Wannan ya zarce duk abin da mu ka taba samu tun da ake annobar.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here