LABARAI DA DUMI-DUMI: Wasu Batagari Sun Sace Sandar Girman Oba na Legas
Rahotanni daga jihar Legas na cewa wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai hari gidan Oba na Legas inda suka ɗauke sandan girmansa, kamar yadda jaridar TheCable a Najeriya ta ruwaito.
Read Also:
Sandan ita ce alamar mulki ko kuma ƙarfin mulkin Oba na Legas wanda shi ne sarkin garin.
Rahotannin sun bayyana cewa ‘yan daban sun kutsa gidan sarkin ne duk da sojojin da aka jibge da aka ajiye a gidan.
An kuma bayyana cewa ‘yan daban sun yi niyyar ƙona gidan sarkin ne amma sojoji sun yi ƙoƙarin dakile yunƙurin nasu