Saudiyya:  Allah-Wadai da Zanen ɓatancin Annabi Muhammad SAW

 

  Ƙasar Saudiyya ta yi Allah-wadai da zanen barkwancin da ake kallo a matsayin ɓatanci ga Manzon Allah SAW, da aka yi a Faransa.

  Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar ta yi kakkausar suka ga duk wani yunƙuri na danganta ta’addanci da addinin Musulunci.

  Sanarwar ta buƙaci a kaucewa tsokana, da cin mutuncin wani addini da sunan ‘yancin faɗin albarkacin baki.

  ”Muna Allah wadai da duk wani zane da aka yi don ɓata sunan Annabi SAW,sannan muna Allah wadai da duk wasu ayyukan ta’addanci ko su wane ne suka aikata su” in ji sanarwar.

  Ƙasashen Musulmai da dama sun ƙaurace wa kayayyakin da Faransa ke sayarwa, a wani ɓanagare na nuna fushi kan matakin Shugaba Emmanuel Macron na kare zanen da aka yi

  Tuni an fara cire kayan da Faransa ke samarwa a wasu shaguna da ke Kuwait da Jordan da kuma Qatar.

Haka ma an gudanar da zanga-zanga a Libiya da Syria da kuma Zirin Gaza.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here