Kasashen Duniya 13 da Kasar Saudiyya ta na Zuwa Aikin Umrah

Hukumomi a kasar Saudiyya sun hana wasu kasashen duniya 13 zuwa aikin umrah.

Saudiyya tace an ɗauki wannan matakin ne saboda yadda cutar COVID19 ke cigaba da yaɗuwa a kasashen.

Hakanan Saudiyya tace duk wanda yaje waɗannan kasashen to ya killace kanshi na mako 2.

Hukumar dake kula da masallatai biyu masu tsarki a kasar Saudiyya ta bayyana sunayen wasu kasashe 13 da ba’a amince su je aikin umrah da aka buɗe kwanan nan ba.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da shafin Haramain Sharifain na dandalin sada zumunta facebook ya fitar ranar Laraba.

A jikin takardar, Saudiyya ta bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne saboda karuwar masu harbuwa da cutar COVID19 a kasashen.

Hakanan kuma Saudiyya tace ba wai aikin Umrah kaɗai aka hana mutanen waɗannan ƙasashen ba harda shiga ƙasa baki ɗaya.

Wane kasashe ne hanin ya shafa?

Kasashen da wannan hanin ya shafa sun haɗa da Afghanistan, Argentina, Brazil, Masar da Habasha

Sauran sune, Indiya, Indonesia, Lebanon, Pakistan, Afirka Ta Kudu, Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Wani ɓangaren takardar, tace: “Duk mutanen da suke son shiga Saudiyya da suka je wadannan kasashen, sai sun killace kansu na makwanni 2, kafin su fara batun zuwa kasa mai tsarki.”

“Ma’aikatar cikin gida na cigbaa da bibiyar kasashen duniya kan yaɗuwar cutar korona, kuma za’a iya ƙara wasu kasashen nan gaba ba tare da sanarwa ba.”

Saudiyya ta shawarci musulmin duniya da su ziyarci ofishin jakadamcinta dake kasashen su domin sanin ko kasar su na cikin hanin kafin su ɗaura ɗamarar tafiya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here