Kasar Saudiyya ta Hana Kai-kawon Jiragen Sama da na Ruwa

Kasar Saudiyya ta dakatar da zirga zirgar jiragen sama da ruwa daga kasashen waje.

Hakan na zuwa ne a matsayin mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu.

A baya bayan nan an samu bullar sabon nau’in korona mai hatsari a Landan da ke bazuwa.

Kasar Saudiyya a ranar Asabar, ta dakatar da shigowar jiragen tare da dakatar da shiga kasar ta kasa ko jiragen na akalla mako guda, bayan samun karin yaduwar cutar korona a Birtaniya, The Punch ta ruwaito.

Masarautar ta “dakatar da tashi da saukar jirage sai idan da bukata ta musamman na tsawon sati daya, wanda za a iya tsawaita dokar da karin sati guda,” a cewar SPA, lokacin da ake shaidawa ministan harkokin cikin gida.

Dakatarwar bata shafi jirgin yakin da ke masarautar ba, wanda za a amince ya tafi, a cewar SPA.

Dokar na zuwa ne bayan kasashen turawa da dama sun hana shiga kasashen su daga Ingila a ranar Lahadi bayan gwamnatin kasar Birtaniya ta bayyana cewa sake ballewar cutar “ya wuce gona da iri”.

A cewar SPA, fasinjojin da suka zo daga nahiyar Turai, ko duk wata kasa da aka sake samun bullar cutar, tun daga ranar 8 ga Disamba akwai bukatar su killace kansu na tsawon sati biyu, kuma ayi musu gwaji.

Kasar Kuwait ma ta sanar da dakatar da shigowar fasinjoji daga Birtaniya sakamakon sake bullar cutar.

Ana kara samun yaduwar cutar a nahiyar Turai, yayin da a satin da ya gabata yankin ya zama na farko a duniya da aka rasa rayuka fiye da 500,000 sakamakon COVID-19, bayan alkaluma sun nuna cewa cutar ta sake kunno kai a sassan Birtaniya.

A satin da ya gabata, kasar Saudiyya ta gudanar da rigakafin corona, bayan da rigakafin Pfizer/BioNTech ya isa kasar a Karon farko.

Saudiyya ta samu fiye da mutum 361,000 da suka kamu da cutar, tare da rasa rayuka fiye da 6000, inda tafi duk sauran kasashen Larabawa. Haka kuma ta fi yawan wadanda suka warke.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here