Sojoji Sun Ceto Mutane 7 da aka Sace, Sun Kashe Ƴan Bindiga 3 a Kaduna

 

Jihar Kaduna – Sojoji sun bindige ƴan bindiga uku a wani samame a maɓoyarsu da ke jihar Kaduna.

Dakarun sojojin sun kuma ceto mutum bakwai daga hannun ƴan bindigan a maɓoyarsu da ke ƙauyen Kurmin-Kare cikin ƙaramar hukumar Kachia.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ƴan bindigan sun sace makiyaya uku da suka je sayar da shanunsu tare da wasu mata huɗu lokacin da suke dawowa daga kasuwa.

Yadda sojoji suka fatattaki ƴan bindiga

Wani ɗan banga wanda yana ɗaya cikin waɗanda suka jagoranci sojoji zuwa sansanin ƴan bindigan, ya ce an kai samamen ne da ƙarfe 4:12 na yammacin ranar Asabar.

Ƴan bayyana cewa ƴan bindigan sun gudu sun bar mutanen ne bayan jami’an tsaron sun buɗe musu wuta.

Wani shugaban al’umma a yankin ya tabbatar da ceto mutanen guda bakwai daga hannun ƴan bindigan.

“Eh da gaske ne sojoji kun kuɓutar da wasu Fulani ciki har da mata waɗanda ke dawowa daga kasuwar ƙauyen SCC da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su.”

– Wani shugaba

Ya bayyana cewa tun da farko ƴan bindiga sun buƙaci a ba su N30m a matsayin kuɗin fansa, inda ya ƙara da cewa sun ƙwace kuɗi masu yawa a hannun Fulanin.

Me jami’an tsaro suka ce kan lamarin?

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa a jira shi zai sake kiran wayarmu daga baya.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here