Sojoji Sun Kashe Wadanda Suke Kai wa ‘Yan ISWAP Kayayyakin Bukata 28 a Garin Kukawa da ke Borno

 

Dakarun sojojin Najeriya sun sheke rayuka 28 na wasu da ke kai wa ‘yan ta’addan ISWAP kayayyakin bukata.

Majiyar tsaro ta ce wadanda aka yi wa luguden wuta masu kai wa ‘yan ta’addan makamai, man fetur da kasuwancin.

Har ila yau, masuntan da aka sheke duk masu hada kai da ‘yan ta’addan ne kuma an haramta kamun kifi a kogin.

Kukawa, Borno – A kalla ‘yan ta’adda 28 da ke da alaka da Islamic State of the West African Province (ISWAP) tare da masu basu hadin kai a kasuwancin kifi ne suka hadu da ajalinsu a ranar Lahadi, PRNigeria ta tattaro hakan daga majiyoyin sirri.

Majiyoyin da aka tura yankin arewa maso gabas a jahar Borno, sun ce mayakan da masu basu hadin kai da suka hada da masunta an kashe su ne sakamakon shiryayyen harin dakarun kasa da na sama wanda sojojin suka hada a Daban Masara da ke karamar hukumar Kukawa ta jahar.

PRNigeria ta tattaro cewa, bayan bayanan sirrin da aka samu har aka kai farmakin, an yi nasarar sheke miyagu ashirin da ke taimaka wa ‘yan ta’addan da kayayyakin bukata.

Daban Masara na nan a arewacin tsakar dajin Chadi, kusan tafiyar sa’o’i biyu daga garin Kukawa.

Kamar yadda majiyar rundunar sojojin ta ce, wurin an saba ganin ‘yan ta’adda wanda kuma ya zama wurin haduwarsu domin karbar makamai, man fetur, kayan abinci, babura da sauran ababen bukata da ake kai musu.

“A wurin babu masu gidaje ko kuma jama’a kuma an haramta wa masunta zuwa wurin. Wurin zaman ‘yan ta’adda ne, abokan su da ma’aikatansu a kasuwancin kifi.

“Wasu daga cikin mayakan ta’addancin da ke wurin an ajiye su ne kawai suna jiran umarnin shugabanninsu domin kaddamar da hari kan sojojin da ke wurin,” yace.

Majiyar ta kara da cewa mayakan da yawa da suka samu rauni a ranar Lahadi sun ki zuwa asibiti domin neman lafiya saboda tsoron kada a cafke su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here