Taliban: Ƙungiyar ta Amince ta yi Aiki da Yarjejeniyar da ta ƙulla da Amurka
Ƙungiyar Taliban ta ce ta amince Amurka ta yi aiki da yarjejeniyar zaman lafiyar da suka yi a bara.
Wannan na zuwa ne bayan ganawar gaba da gaba ta farko tsakanin ɓangarorin biyu tun bayan da ƙungiyar ta ƙwace iko da Afghanistan a watan Agusta.
Wakiliyar BBC ta ce Amir Khan Muttaqi shi ne muƙaddashin ministan harkjokin waje na gwamnatin Taliban kuma shi ya jagoranci ƴan ƙungiyar a Doha. Ya ce yana so ya inganta alaƙarsu da sauran ƙasashen duniya.
Yarjejeniyar ta ƙunshi alƙawarin da Ƙungiyar Taliban ta ɗauka na hana al-Qaeda aiki a yankunanta.
Tattaunawar, wadda aka yi a Doha, wani ɓangare ne na ƙoƙarin da Taliban ke yi na ganin ƙasashen duniya sun san da ita.
Amurka ta jaddada cewa tattaunawar ba ta duba batun ayyana ƙungiyar a matsayin halattacciya ba.