Elon Musk: Kadan Daga Tarihin Wanda Yafi Kowa Kudi a Duniya

 

A ranar Alhamis, 7 ga watan Junairu, 2021, aka tabbatar da cewa Elon Musk ya zama mutumin da ya fi kowa arziki a fadin Duniya.

Legit.ng Hausa ta tattaro maku kadan daga cikin tarihin Elon Musk mai shekaru 49 daga shafin Britannica.

1. Kuruciya

An haifi Musk ne a watan Yunin 1971, mahaifin Elon Musk mutumin kasar Afrika ta kudu ne, mahaifiyarsa kuma ta fito daga Kanada, daga baya iyayensa sun rabu da juna, ya cigaba da zama a Pretoria.

A shekarar 1988 Musk ya samu takardar zama ‘dan kasar Kanada, ya bar Afrika ta kudu, a wancan lokaci ne ya tattara ya koma Amurka.

2. Karatu

Musk ya yi karatu ne a jami’ar Queen’s University ta Ontario. A 1992 ya koma jami’ar University of Pennsylvania a Philadelphia ya samu Digiri a ilmin tattalin arziki da kimiyya. A 1997 ya nemi ya fara digirgir a jami’ar Stanford University, amma sai ya watsar.

3. Kirkire-kirkire

Tun ya na shekara 12, Elon Musk ya kirkiro fasahar wasanni watau ‘Video Game’ da ya saidawa wani kamfani.

Bayan wasu ‘yan shekaru sai ya kafa kamfanin Zip 2, daga baya Compaq sun saye wannan kamfani a kan $300m.

Ana tafiya sannu a hankali sai Musk ya kafa kafanin X.com, wanda ya zama PayPal. A 2002 ya saye kamfanin eBay.

A shekarar 2002, Musk ya kai ga bude kamfanin jiragen sama-jannati na SpaceX, bayan shekaru hudu ya fara kirkiriran jirgin Falcon 1.

Daga baya Musk ya yi ruwa da tsaki wajen kafa kamfanin Tesla masu yin motocin da ke amfani da lantarki.

4. Aure

Attajirin ya hadu da mai dakinsa Justine Wilson a lokacin da suke karatu a jami’a. Daga baya sun rabu bayan ‘ya ‘ya biyar sun shiga tsakaninsu.

A 2008 Musk ya hadu da Talulah Riley, bayan ‘yan shekaru suka yi aure. A 2012 masoyan suka rabu da juna, amma daga baya su ka sake aure.

A 2014 sai aka ji Musk yana neman rabuwa da Riley, sai maganar ta mutu. A 2016 sakin ya tabbata, attajirin ya sake sakin sahibar ta sa.

A 2018 ne Musk ya auri wata Mawakiya mai suna Grimes wanda ta haifa masa wani yaro da aka sanyawa suna ‘X Æ A-12.’

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here