Shugaba Tinubu ya Amince da N70,000 a Matsayin Mafi Karancin Albashi ga Ma’aikatan Najeriya

 

Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya, inda ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin albashi na kasa duk bayan shekaru uku.

Mohammed Idris, ministan yada labarai ne ya sanar da hakan a fadar shugaban kasa dake Abuja, ranar Alhamis.

A cewar Idris, shugaban ya bayyana hakan ne a ci gaba da ganawa da shugabannin kungiyar kwadagon.

Comrade Joe Ajaero, shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, da Comrade Festus Usifo, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa (TUC), na cikin taron tare da wasu mambobin kungiyarsu.

Kafin taron dai shugabannin kwadagon sun dage akan biyan mafi karancin albashi na N250,000.

Cikakkun bayanai daga baya…

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here