Shugaba Tinubu na Ganawar Sirri da Manyan Hafsoshin Tsaron Nigeriya 

 

FCT Abuja – Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na ganawar sirri yanzu haka da manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan a Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja.

Taron dai na gudana ne karkashin majalisar tsaro ta Najeriya a fadar shugaban ƙasa yau Litinin, 5 ga watan Agusta, 2024 yayin da ake tsaka da zanga-zanga.

Babban hafsan tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa ne ya jagoranci hafsoshin tsaro da sauran shugabannin hukumomin tsaro zuwa taron, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da matasa ke ci gaba da gudanar da zanga-zangar adawa manufofin gwamnatin Tinubu da suka kawo da yunwa a kasar.

A jiya Lahadi, shugaban ƙasa ya yi jawabi kai tsaye ga ƴan Najeriya kan halin da ake ciki, inda ya buƙaci a dakatar da zanga-zangar da aka fara.

Bola Tinubu ya bayyana cewa ba zai zauna ya naɗe ƙafa yana kallon wasu tsiraru da ƴan adawa suka ɗauko haya su ruguza zaman lafiya ba. Ya kuma tabbatarwa masu zanga zangar cewa ya ji duka kokensu tare da gargaɗin cewa ba zai bari a ci gaba da asarar rayuwa da dukiyoyi ba.

A halin yanzu dai mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila sun halarci taron tsaron yau Litinin.

Sauran mahalarta taron sun haɗa da Sufeto Janar na rundunar ƴan sanda, IGP Kayode Egbetokun da sauran shugabannin hukumomin tsaro, Daily Trust ta rahoto.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here