EndSars: Ƴan Sandan Lagos sun Buɗe Wuta ga Dubban Jama’a masu zanga-zanga a Jahar Ta su.
Ƴan sandan kwantar da tarzoma sun buɗe wa dubban masu zanga-zangar EndSars wuta a dandalin Lekki toll gate da ke birnin Legas a kudancin Najeriya da yammacin Talata.
Masu zanga-zangar sun ci gaba da yin ta ne bayan da gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a jihar a ranar Talata da safe sakamakon ƙona wani ofishin yan sanda da aka yi.
BBC tana cikin nuna bidiyon ci gaban zanga-zangar kai tsaye a shafinta na Facebook a lokacin da aka fara harbe-harbe da bindiga a wajen.
Dubban mutane ne suka sake taruwa a dandalin na Lekki toll gate suna ci gaba da zanga-zangar.
Read Also:
Amma nan da nan sai komai ya hargitse wajen ya cuɗe. Babu tabbas kan ko mutum nawa ne suka jikkata a lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 6.45 na yamma agogon Najeriya.
Tuni dai zanga-zangar ta rikiɗe zuwa rikici tsakanin masu yin ta da wasu da ake zargin ƴan daba ne a wasu manyan biranen ƙasar da suka haɗa da babban birnin tarayya Abuja.
Wakilin sashen BBC Pidgin ya ce ya ga mutum ɗaya da ya jikkata.
Tuni a wasu jihohin ma aka sanya dokar hana fita ta sa’a 24 kamar Jos da Ekiti da Abia.
Dama tun da farko a ranar Talatar Babban Sifeton ‘yan sandan Najeriya ya umarci baza ‘ƴan sandan kwantar da tarzoma a duk faɗin ƙasar.
Sanarwar Muhammad Adamu, na zuwa ne yayin da ake samun ƙaruwar tashin hankali a wasu jihohi sakamakon zanga-zangar nuna adawa da cin zalin da ake zargin jami’an ‘yan sanda na yi.