‘Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Wani Hakimi da Yaransa

Ƴan bindiga sun tafi gidan hakimin garin Matseri a Jihar Zamfara sun yi awon gaba da shi.

Ƴan bindigan sun kuma sace yaran hakimin guda hudu a lokacin da suka tafi sace shi.

Har wa yau, sun kashe wani mazaunin garin da ya yi ƙoƙarin taka musu birki ya ceci hakimin Wasu ƴan bindiga sun sace hakimin garin Matseri na da ke ƙaramar hukumar Anka a Zamfara, Alhaji Halilu Matseri da yaransa huɗu Sun kuma kashe wani Maigaiya Matseri da ya yi ƙoƙarin ceto hakimin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Sarkin Anka wadda shine shugaban kwamitin sarakuna na jihar, Alhaji Attahiru Ahmed ya ce,”Ƴan bindigan sun afka garin a safiyar ranar Laraba inda suka yi awon gaba da hakimin da ƴaƴansa huɗu.”

Wani mazaunin garin, Mallam Mohammed Musa ya ce ƴan bindigan sun taho garin a kan babura misalin kaɍfe 2 na dare.

“Sun zo a kan babura sannan suka wuce gidan hakimin kai tsaye inda suka yi awon gaba da shi da yaransa guda huɗu. Rundunar ƴan sandan Jihar ba tayi tsokaci kan lamarin ba a lokacin haɗa wannan rahoton.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here