Manyan Tsagerun ‘Yan Bindiga 4 Sun Shiga Hannu a Jahar Sokoto

 

Wasu mutum hudu da ake zargin manyan tsagerun yan bindiga ne sun shiga hannu a jahar Sokoto.

Kwamandan rundunar NSCDC yace an gayyaci wani babban mutum wanda ake zargin yana da alaka da ɗaya daga cikin waɗanda aka kama.

Rahoto ya tabbatar da cewa daga cikin mutanen da suka shiga hannu akwai yan leken asirin yan bindiga.

Sokoto- Haukumar tsaro (NSCDC), ranar Laraba, ta sanar da kame wasu tsagerun yan bindiga guda huɗu a jahar Sokoto.

Channelst tv ta rawaito cewa waɗan da ake zargin mambobin manyan ƙungiyoyin yan bindiga ne da suka addabi jahohin Sokoto da Zamfara.

Jami’ai sun damke mutanen ne bisa zargin hannu a garkuwa da manyan mutane, fashi da makami, satar dabbobi da kuma kashe mutane a wasu yankunan waɗan nan jahohi biyu.

An gayyaci wani babban mutum

Kwamandan jami’an NSCDC reshen jahar Sokoto, Mohammed Saleh-Dada, yace wasu daga cikin mutanen da aka damke yan leken asirin yan bindiga ne.

A cewar kwamandan hukumarsu ta gayyaci wani babban mutum da ake zargin yana da alaƙa da ɗaya daga cikin mutanen da aka kame.

Yace:

“Mun gayyaci wani sanannen mutum a yankin karamar hukumar Dange/Shuni, jahar Sokoto, bisa zargin yana da wata alaƙa da mutum daya da ake zargi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here