Kashe Sojoji: ‘Yan Najeriya Sun Nuna Bacin Rai Kan Bidiyon da ke Yawo a Shafukan Sada Zumunta
Wani bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta yana nuna gawawwakin sojojin da aka ba da rahoton cewa ‘yan bindiga ne suka harbe a kudu maso gabashin Najeriya ya janyo bacin rai a kasar.
Bidiyon maras dadin gani wanda ga alama an dauke shi ne bayan harin da aka kai ya nuna mutane zagaye da wani abu mai kama da motar jami’an tsaro an dambara rubutun “Sojoji” a kowanne bangare.
Read Also:
An ga gawawwaki guda biyu kwance shame-shame a kasa, sai kuma gawa biyu a mota male-male da jini.
Ba a tabbatar da kafar da ta fara yada bidiyon ba zuwa yanzu.
Rundunar soji da ta ‘yan sanda ba su fitar da wata sanarwa ba game da lamarin.
Sai dai gwamnan jihar Anambra ya yi alla-wadai da harin a kan sojoji.
Mutane sun bayyana damuwa da takaici a kan karuwar hare-haren da akasari ake far wa hukumomin tsaro da jami’an gwamnati da cibiyoyin hukuma.
Kafofin yada labarai sun ruwaito cewa ‘yan bindiga sun kashe sojoji guda hudu da kuma wani farar hula a lokacin harin na ranar Laraba a jihar Anambra ta kudu maso gabas.