Kashi 20 Cikin ‘Yan Najeriya ba su da Wayoyin Komai da Ruwanka – UNICEF
Sama da kashi 50 cikin 100 na ‘yan Najeriya ba su da damar samun intanet, yayinda kashi 20 ba su da wayoyin komai da ruwanka, wato smart phones, wanda ke haifar da wagegen gibi a cewar UNICEF.
UNICEF ta kuna nuna damuwa kan yada ake samun karuwar yara mata miliyan 1.3 da ke barin makaranta a kowace shekara.
Mataimakin UNIICEF a Najeriya, Rushnan Murzata, ta ce runguwar fasahar zamani da ilimi na da muhimmanci a wannan gabar ta rayuwa.
Murtaza ta ce akwia bukatar kara himmatuwar gwamnatoci domin cire wannan tazara da sake ceto rayuwa mata.