Goyon Bayan Sojoji: ‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-Zangar a Sudan
Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga zanga da ke goyon bayan sojoji, wadanda suka taru a rana ta uku a Khartoum.
Masu boren na kira a maye gurbin gwamnatin riko, wadda suka ce ita ce ta fi dacewa wajen tunkurar rikicin siyasa da na tattalin arzikin kasar.
Read Also:
Rahotanni sunce masu zanga zangar sun taru a gaban gidan Shugaban kasa suna kiran a kifar da gomnatin riko.
Firaminista Abdalla Hamdok ya yi taron gaggawa da majalisar ministocinsa, inda ya bayyana tashin hankalin a matsayin rikicin da yafi kowane tun bayan da aka kifar da gwamnatin tsohon Shugaba Omar Albashir shekaru biyu da suka gabata.
Sai dai masu suka sun ce jami’an tsaro ne suka shirya zanga zangar domin kawo cikas ga kokarin da ake yi don mayar da kasar kan tafarkin mulkin dimokradiyya.