Kebbi: Uwargidan Gwamnan ta yi Martani Mai Zafi ga Wani Matashi

Matar mai girma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudo ta mayar da martani ga wani a Twitter, bayan yayi mata tsokacin da taga bazata iya kyalesa ba

Ta wallafa hotunan wasu kwamishinonin jihar Kebbi masu kananun shekaru a ranar matasa ta kasa, inda tace yakamata a dinga ba matasa dama – Sai saurayin yace ai daga gani ‘yan uwan gwamnan ne, shine tace eh! ‘Yan uwanta ne, Idan ya samu irin wannan damar ya dora makiyansa.

Najeriya tayi shagalin zagayowar ranar matasa ta kasa a ranar 1 ga watan Nuwamba. Don nuna farinciki, matar gwamnan jihar Kebbi, Zainab Bagudu ta wallafa hotuna 5 na kwamishinonin jihar masu karancin shekaru, inda take nuna basu wuce shekaru 30 zuwa 40 ba don bunkasa kasa.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitterr: “A jihar Kebbi, Gwamna Atiku Bagudu ya zabi kwamishinoni da ke tsakanin shekaru 30 zuwa 40. Najeriya za ta samu cigaba ne idan aka bai wa matasa dama. Barka da ranar matasa ta kasa.”

Bayan wannan wallafar ne wani yayi tsokaci a kai, inda ya ce ya san kwamishinonin da mijinta ya zaba ‘yan uwa ne da abokan arzikinsa.Bayan ganin wannan tsokacin ne ta mayar masa da martani, inda ta rubuta: “Eh. Iyayena da iyayensu uwa daya uba daya suke. Idan ka samu dama irin wannan, ka zabo makiyanka ka dora.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here