Corona: Hukumar Lafiya ta Duniya ta Bayyana Cewa Afirka ce Koma Baya Wajen Karbar Rigakafin Annobar
Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta gargadi cewa an bar Afirka a baya wajen karbar rigakafin annobar corona.
Read Also:
A lokacin wani jawabi ga manema labarai, Dr Tedros Adganom Ghebreyesus ya ce ƙasashen Afirka biyu kaɗai ne suka cimma kashi 40 cikin 100 na al’ummar da WHO ke fatan ganin an yi wa rigakafi zuwa karshen 2021.
Ya ce wannan adadi shi ne mafi kankanta ga kowanne yanki.
Dr Tedros ya ce sama da allura biliyan 5.7 aka fitar a duniya, sai dai kashi 2 cikin 100 na wannan adadin nahiyar Afirka ta samu.
Ya yi gargadi cewa idan ba a kasafta rigakafin yada ya dace ba annobar za ta sake dawo wa.