Cutar Corona za ta Daina Barazana ga Lafiyar Al’umma a Bana – WHO
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce yana da kwarin gwiwa a wannan shekarar zai ayyana cutar corona a matsayin annobar da ba ta kai matakin barazanar lafiya ga alummar duniya ba.
Read Also:
Michael Ryan, daraktan sashen ayyukan gaggawa na hukumar WHO ya ce, hukumomin lafiya da dama za su kai matakin da za su bayyana annobar a matsayin barazana ga lafiya wadda za ta ci gaba da kashe rayuka, amma ba za ta iya katse harkokin yau da kullum ba.
Mista Ryan ya ce, za a iya bayyana cutar tamkar wani nau’i ne na mura.
Annobar corona ta hallaka dubban al’umma a sassan duniya tun bayan barkewar ta a farkon shekarar 2020.